Gwamnatin jihar Bauchi ta ce a kowace rana tana kashewa kowane mai cutar Korona da aka killace ₦4500 a matsayin kudin abinci.

Rilwanu Muhammad, shugaban hukumar bunkasa lafiya a matakin farko ta jihar shi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na NAN.

Ya ce gwamnan jihar, Bala Muhammad shi ne ya amince da kudin domin tabbatar da cewa an bawa kowane mai dauke da cutar ingantancen abinci.

Mohammed wanda shi ne shugaban kwamitin kwakkwafi da kuma lalubo masu dauke da cutar a jihar Bauchi ya ce gwamnan ya bawa jami’an gwamnati umarni da su tabbata marasa lafiya sun ji su tamkar a gida yayin da suke cibiyoyin.