Kowace jiha ta cancanci a samar da Ruga – Bodejo


Abdullahi Bodejo, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa baki daya ya ce kowace jiha a kasarnan ta cancanci a samar mata da Ruga.

A wata tattaunawa da jaridar The Sun Bodejo ya ce Fulani sune kabila mafi yawa a Najeriya kuma ya kamata a basu wurare su zauna ko ina a fadin kasarnan.

Ya kuma shawarci gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum da ya cika alkawarin da ya dauka na bawa fulani makiyaya wani bangare na dajin Sambisa.

“Idan gwamnan Borno ya ce ya bawa Fulani dajin Sambisa suje su zauna yakamata ya aiwatar da haka amma kada batun ya zama siyasa,” ya ce.

“Fulani a shirye suke su karbi ba wai Sambisa kadai ba kowace jiha a kasarnan ya kamata ta bawa Fulani wani dan wuri su zauna tunda sune kabila mafi yawa a Najeriya.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like