Kotun zaben shugaban kasa za ta yanke hukunci ranar Laraba


Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta tsayar da gobe ranar Laraba, 11 ga watan Satumba a matsayin ranar yanke hukunci karar da jam’iyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar suka shigar inda suke kalubalantar nasarar da shugaban kasa Muhammad Buhari ya samu.

Daraktan sadarwa ta kotun daukaka karara ta tarayya, Sa’adatu Musa ita ta sanar da haka ranar Talata.

Jama’a da dama sun zuba ido dan ganin yadda hukuncin na gobe zai kaya.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like