Kotun Shari’ar Musulunci A Kano Ta Aikawa Da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Sammaci


Alkalin kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Shahuci a jihar Kano, Malam Garba Kamilu ya ba da umurnin a ‘lika wa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sammaci a kofar dakinsa, ko kuma duk wani waje da dole zai gani sakamakon yaki yarda a hadu da shi a mika masa takardar sammaci.

Sheikh Dauda Lokon Makera ne dai ya yi karar Sheikh Daurawa bisa wasu tuhume-tuhume da yake masa a kan shirin Tambaya Mabudin Ilimi.

Shirin Tambaya mabudin Ilimi dai ne shiri ne da ya yi fice a gidajen Radiyon kasar nan da shekh Dauda yake ikirarin shi ne ya kirkiro shirin.

Inda sheikh Dauda lokon makera yake ikirarin shine asalin Wanda ya kirkiro Shirin Amma sheikh daurawa yake amfani da Shirin bada izininsa ba har takai da yabuga faifan sidi da littafi na Shirin batare da izinin saba A matsayinsa na mamallakin shirin, A cewa sheikh Dauda lokon makera Wanda yayi ‘karar sheikh Aminu Daurawa


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like