Kotun koli ta tabbatar da zaben Yahaya Bello


Kotun koli ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya samu a zaben da aka gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba.

Dukkanin alkalai 7 da suka saurari karar sun yarda cewa dauka karar da dantakarar jam’iyar PDP, Musa Wada yayi bata taso ba saboda rashin isassun hujjoji.

Mai shari’a, Uwani Abba Aji ce ta karanta hukuncin kotun a madadin sauran.

Ta bayyana cewa masu kara sun gaza tabbatar da zargin da suke cewa an samu tashin hankali tare da kada kuri’a fiye da ka’ida da kuma kin yin amfani da na’urar card reader.

Kungiyoyin farar hula da dama sun yi allawadai da yadda aka gudanar da zaben mai cike da rikici.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like