Kotun koli ta tabbatar da hukuncin soke zaben fidda gwanin jam’iyar APC a jihar Rivers


Kotun koli ta tabbatar da hukuncin soke zaben fidda gwani da kuma na shugabannin jam’iya da wani tsagi na jam’iyar APC ya gudanar a jihar Rivers.

Wata babbar kotu ce dake zamanta a Fatakwal babban birnin jihar ce ta soke zabukan da aka gudanar wanda tace cike yake da kura-kurai da kuma rikici.

Mai shari’a, Muhammad Dattijo shine ya jagoranci rukunin alkalan su biyar da suka yanke hukuncin.

Hakan na nufin dai jam’iyar ta APC baza ta tsayar da yan takarkaru ba a zabuka masu zuwa.

A jiya ne dai jam’iyar APC reshen jihar ta nemi hukumar zabe ta dage zabukan da za ta gudanar a jihar domin bawa yan takararta damar yin yakin neman zabe.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like