Kotun koli ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka ta yanke da ya daure tsohon gwamnan jihar Taraba,Jolly Nyame na tsawon shekaru 12 a gidan yari.

Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ita ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotun inda take zarginsa da yin amfani da ofishinsa ta hanyar da bata da ce ba.

Ana zarginsa da karkatar da kudade da yawansu ya kai naira biliyan ₦1.64 lokacin da yake mulkin jihar Taraba daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Bayan da ya shafe shekaru sha biyu yana fuskantar shari’a , a ranar 30 ga watan Mayu na shekarar 2018, alkalin babbar kotun birnin tarayya Abuja,Adebukola Banjoko ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari

Rashin gamsuwa da hukuncin ne ya sa tsohon gwamnan garzaya kotun daukaka kara inda ta rage hukuncin da aka yanke masa ya zuwa shekaru 12.

Duk da haka bai gamsu ba sai da ya nufi kotun koli inda yake kalubalantar hukuncin.