Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Tsohon Ministan Neja-Delta Mista OrubebeTsohon Ministan Neja-Delta lokacin Shugaba Goodluck Jonathan wato Godsday Elder Orubebe ya sha a Kotu inda aka wanke shi tas daga zargi. 

Hakan dai na zuwa ne bayan Kotun CCT ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.

Da fari dai Alkali Danladi Umar na Kotun CCT ya bayyana cewa Orubebe ya ki bayyana wasu kadarorin da ya mallaka don haka ya aikata laifi. 

Sai dai yanzu Kotun daukaka kara ta Abuja tace sam Mista Orubebe bai yi wani laifi ba.

Alkali Abdu Aboki ya bayyana cewa tsohon Ministan ya riga ya saida kadarorin da ake magana tuni don haka babu dalilin kama shi. 

Wasu dai na ganin cewa shirin yaki da cin hanci da Gwamnatin Buhari take yi na gamuwa da matsala tun da aka wanke Bukola Saraki ga shi a lokaci guda kuma an wanke Orubebe.

Comments 0

Your email address will not be published.

Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Tsohon Ministan Neja-Delta Mista Orubebe

log in

reset password

Back to
log in