Kotun Da’ar Ma’aikata Ta Kori Karar Saraki Ta Kuma Wanke Shi Daga Dukkanin Zargin Da Ake Masa 


Kotun tabbatar  da da’ar ma’aikata ta kori karar da akewa shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki,kan zargin da ake masa nayin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka. 

Tun a ranar 4 ga watan Mayu ne Saraki ya nemi kotun da tayi watsi da tuhumar da ake masa bayan da masu gabatar da kara suka rufe gabatar da hujjojinsu. 

A hukuncin kotun na yau Alkalin kotun,Danladi Umar yace masu gabatar da kara sun gaza wajen gamsar da kotu zarge zargen da akewa Saraki. 

Comments 0

Your email address will not be published.

Kotun Da’ar Ma’aikata Ta Kori Karar Saraki Ta Kuma Wanke Shi Daga Dukkanin Zargin Da Ake Masa 

log in

reset password

Back to
log in