Kotu ta yi barazanar tasa keyar shugaban DSS ya zuwa gidan yari


Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja tayi barazanar tsare, Yusuf Magaji Bichi shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS a gidan yari kan cigaba da tsare,Omoyele Sowore da kuma wani mai fafutuka, Olawale Bakare.

Alkalin kotun mai shari’a, Ijeoma Ojukwu itace ta bayar da wannan umarnin ranar Litinin.

Tun da fari mai shari’ar ta sanar da hukumar ta DSS kan illar dake tattare da bijirewa umarnin kotu.

Hukumar DSS ta kama Sowore ranar 3 ga watan Oktoba kuma tun wancan lokacin take tsare da shi duk da belinsa da kotu ta bayar har karo biyu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like