Kotu ta yankewa Ronaldo hukuncin zaman gidan yari na shekara 2


Wata kotu a kasar Spain ta yankewa Christiano Ronaldo daurin shekaru biyu a gidan yari.

Amma kuma Ronaldo ya amince da hukuncin zaman gidan yarin, domin sasanta batun rikicin kaucewa biyan kudin haraji.

A zahirance Ronaldo ba zai yi zaman gidan yarin ba saboda bai taba aikata wani laifi ba amma hukumomin kasar za su saka masa ido har zuwa tsawon shekaru biyu domin a tabbatar bai sake aikata laifi makamancin haka.

Masu gabatar da kara na kasar ta Spain na tuhumar tauraron dan wasan na kulob din Real Madrid da laifin kaucewa biyan kudin haraji da yawansu ya kai miliyan €14.8 .

Ronaldo ya musalta zargin da ake masa lokacin da ya bayyana a gaban kotu lokacin bazara a shekarar da ta wuce amma har ya zuwa yanzu ba a sasanta batun ba.

Hukumomi sun yi watsi da tayin da ya yi tun da farko Jaridar El-Mundo ta rawaito cewa Ronaldo ya amince da daurin gidan yarin tare da amincewa da laifin da ake zarginsa.

Haka kuma zai biya kudin tara da yawansu ya kai miliyan €18.


Like it? Share with your friends!

-1
84 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like