Kotu ta umarci INEC ta bawa Okorocha takardar shedar cin zabe


Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta bawa tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shedar cin zabe.

Akalin kotun mai shari’a,Okong Abang ya bayyana cewa tunda har jami’in fadar sakamako ya ayyana Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanata a mazabar yammacin Imo a zaben ranar 23 ga watan Faburairu,INEC bata da dalilin kin bashi shedar cin zabe.

Ya yanke hukuncin cewa matakin kin bawa Okorocha takardar shedar cin zaben ya saba dokokin zabe.

Idan za a iya tunawa hukumar zaben ta cire sunan tsohon gwamnan ne daga cikin jerin wadanda aka zaba bayan da jami’in sanar da sakamakon zaben, Farfesa Francis Ibeawuchi ya ce tilasta masa akayi ya ayyana sunan Okorocha a matsayin wanda ya lashe zaben.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like