Kotu Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Tarayya, Alasan Ado Doguwa


Ado Doguwa shine dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar APC.

Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna yau Litinin ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa, wato Alasan Ado Doguwa. Alasan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya wato mai mukami na uku a majalisar bayan shugaban majalisar da mataimakinsa.

Kotun har wala yau ta ce ta soke zaben da ya kawo Alhassan Doguwa a matsayin dan majalisa a kananan hukumomi biyu. Inda kotun ta bayyana zaben a matsayin mara inganci. Mai shari’a Justice Oludotun Adefope-Okojie, ya ce bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zabe ba zai yiwu ba, domin hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta cire sunayen wadansu jam’iyyun a yayin ayyana sakamakon zaben.

Har wala yau kotun ta ce INEC ta karya doka ta hanyar rubuta sakamakon zaben jam’iyya biyu kawai cikin 53 da suka shiga zaben a fom mai lamba 0EC 8 (II) E. A don haka kotu ta nemi INEC ta sake shirya wani zaben nan da kwana 90 a yankin.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like