Kotu ta soke zaben Dino Melaye


Kotun dake sauraren kararrakin zaben yan majalisar wakilai ta tarayya da kuma yan majalisun dokokin jihar Kogi dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta kori sanata Dino Melaye daga kujerarsa ta wakilcin al’ummar yammacin Kogi a majalisar dattawa.

Kotun ta yanke hukuncin nata ne ranar Juma’a.

Alkalkin dake jagorantar kotun mai shari’a, A.O Chijioke ya umarci hukumar zabe ta INEC da ta gudanar da sabon zabe a mazabar.

Dan takarar jam’iyar APC a zaben,Smart Adeyemi shine ya shigar da kara gaban kotun akan cewa zaben da ya bawa Melaye nasara cike yake da kura-kurai.

Tuni sanata Melaye ya nemi magoya bayansa su kwantar da hankali domin lauyoyinsa za su daukaka kara.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like