Kotu ta sake yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar jifa a Kano


Kasa da kwanaki uku bayan da wata kotun shari’ar Muslunci dake Kano ta yankewa wani mawaki hukuncin kisa kan zargin da ake masa na yin kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) sai gashi wata kotun ta yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rajamu.

Mati Abdu, Dattijo dan shekara 60 an yanke masa hukuncin kan laifin yi wa wata yarinya fyade.

A shekarar 2019 yan sanda suka kama Mati bayan da aka zarge shi da yiwa yarinya yar shekara 12 fyade a kauyen Farsa dake karamar hukumar Tsanyawa ta jihar.

Mai shari’a, Ibrahim Yola na kotun shari’ar Musulunci dake Kofar Kudu kusa da fadar sarkin Kano shi ne ya yankewa Abdu hukuncin kisan.

Mai magana da yawun kotunan jihar, Babajibo Ibrahim ya tabbatarwa da manema labarai yanke hukuncin a ranar Laraba.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like