Kotu ta kori karar dake neman kada a rantsar da Ihedioha


Alkalin Babbar Kotun Tarayya dake Owerri babbar birnin jihar Imo ya kori karar da aka shigar gabansa dake neman a hana rantsar da zaɓaɓɓen gwamnan jihar,Emeka Ihedioha ranar 29 ga watan Mayu.

Rimgim ya ce mai kara wanda shine dantakarar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar DA a zaben 2019 bai cancanci shigar da karar ba saboda magana ce da ta shafi bayan zabe.

Da yake korar kara alkalin ya ce bashi da hurumin ya saurari karar.

Alkalin ya kuma bukaci da a biya wanda aka yi kara zunzurutun kuɗi har miliyan ₦5.

Lauyan wadanda ake kara,Emeka Ihejirika ya ce bayan rashin hurumin sauraran karar da kotun bata da shi masu kara sunci mutuncin ayyukan kotu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like