Kotu ta kori karar dake neman a kori Saraki, Dogara kan sauya sheka


Kotun tarayya dake Abuja tayi watsi da wata kara dake neman a bayyana cewa babu mai wakiltar kujerun kakakin majalisar wakilai Yakubu, shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da kuma wasu yan majalisun tarayya su 54 biyo bayan sauya shekar da suka yi gabanin zaben shekarar 2019.

Da yake ayyana hukuncin, alkalin kotun mai shari’a,Okong Abang ya bayyana cewa kungiyar Legal Defence and Assistance Project (LEDAP) da ta shiga da karar ba ta da ikon shigar kara.

“Mai kara da ya shigar da kara ba jam’iyar siyasa ce ba da ta dauki nauyin takarar yan majalisun.”a cewar Abang.

Har ila yau alkalin ya ce kungiyar ba hukumar zabe ta INEC ce ba dake saka idanu akan ayyukan jam’iyun siyasa da kuma sanya idanu kan zabuka, saboda haka basu da hurumin shigar da wannan kara.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like