Kotu Ta Hana Shekarau Zuwa Umrah


Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta ki amincewa da bukatar Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau na ta bashi fasfo dinsa da ya mallakawa kotun don ya tafi Saudiyya wajen aikin Umra.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Zainab Bage Abubakar ta ce, mallakawa kotu fasfonsa da tsohon Gwamnan ya yi, yana daga cikin sharuddan bayar da belinsa a kan zargin da ake yi masa na karbar Naira milyan 950 daga cikin kudaden yakin neman zaben Jonathan daga hannun Tsohuwar Ministar mai.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like