Kotu ta gaza bayar da belin Fayose


Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi rashin nasara a kokarin da yake na samun beli daga babbar kotun tarayya dake Lagos.

A ranar Litinin, Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFFC ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu inda take masa tuhume-tuhume 11.

Tuhumar da ake wa Fayose sun hada da sata, karbar kudi daga hannun Musliu Obanikoro, mallakar dukiya ta haramtacciyar hanya ta yin amfani da sunan yar uwarsa da sauransu.

Fayose ya ki amincewa da dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa.

Lauyansa Kanu Agabi ya nemi kotun ta bayar da belinsa amma alkalin kotun mai shari’a Mojisola Olatoregun ta sanya ranar Laraba domin duba batun bayar da belin inda ta nemi da a cigaba da tsare Fayose a ofishin hukumar EFCC.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like