Kotu ta dakatar da majalisar kasa daga kwace iko majalisar dokokin jihar Edo


Babbar kotun tarayya dake Abuja ta umarci majalisar dattawa da ta wakilai kan su dakatar da shirin da suke na karbe ikon ayyukan majalisar dokokin jihar Edo.Kotun ta bayar da umarnin ne biyo bayan bukatar da gwamnatin jihar Edo ta gabatar gabanta dake kalubalantar matakin da majalisar dattawa ta yanke.Ranar 30 ga watan Yuli majalisar dattawan ta bawa gwamnan jihar, Godwin Obaseki wa’adin mako guda da ya sake bayar da umarnin kaddamar da kafa majalisar.Obaseki ya ce ba zai bayar da sabon umarnin ba kana ya kalubalanci matakin na majalisar a gaban kotu.Rashin Fahimta tsakanin gwamna, Obaseki da kuma tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya jawo an samu bangarori biyu a majalisar dokokin.


Like it? Share with your friends!

-1
92 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like