Kotu Ta Dakatar Da INEC Gudanar Da Zabe A Mazabun Da Za A Sake Zabe A Adamawa


Wata kotun koli dake Yola ta dakatar da hukumar zabe ta kasa (INEC) daga gudanar da zabe a wuraren da hukumar za ta sake gudanar da zaben gwamna a jihar Adamawa.

Idan ba’a manta ba, jihar Adamawa na daga cikin jihohi shida da hukumar zabe ta ayyana zata sake gudanar da zabe a wasu mazabun jihar.

Alkali Abdul’aziz Waziri ne ya bada umurnin dakatarwar biyo bayan korafin da jam’iyyar MRPD ta yi na cewa ba a sanya alamar jam’iyyar ba a takaddun zabe a zaben gwamna da ya gudana a jihar ta Adamawa.

Sai dai jam’iyyar PDP wacce alkaluma suka bayyana tana da kuri’u mafi rinjaye a sakamakon da hukumar zabe ta fitar ta zargi gwamnan jihar Adamawa kuma dantakaran jam’iyyar APC a zaben gwamnoni, Umaru Jibirilla Bindow da yin amfani da jam’iyyar MRDP don dakatar da karasa zabe a jihar Adamawa.

Amma da aka tuntubi shugaban hukumar zabe na jihar Adamawa Kashim Gaidam dangane da umurnin kotun, Gaidam yace “umurnin kotu baya dakatar da zabe” a saboda haka yace babban ofishin hukumar zabe na kasa ne kawai zata iya magana akan umurnin kotun.

Kafin umurnin kotun, hukumar zabe ta sanya ranar 23 ga watan maris don gudanar da zaben.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like