Kotu Ta Dakatar Da Ganduje Daga Kafa Majalisar Sarakunan Kano


Wata babbar kotun jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a A.T Badamosi, ta dakatar da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, daga kafa majalisar sarakuna da nada membobinta.

A jiya Litinin ne dai gwamna Ganduje ya nada sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban sabuwar majalisar sarakunan Kano da ya kafa bayan kirkirar sabuwar dokar masarautu.

Kotun ta zartar da hukuncin ne a yayin zamanta na ysu Talata.

A wani martani da ya mayar ga kungiyar dattijan jihar Kano da suka nemi ya janye dokar kirkirar sabbin masarautu, Ganduje ya bayyana cewa kungiyar ba za ta iya canja shawarar da ya yanke na kirkirar sabbin masarautu a jihar ba.

A cewar gwamnan, babu abin da zai sauya dokar kirkirar sabbin masarautun tunda dai ta bi dukkan wani matakin doka kafin a tabbatar da ita.

A ranar Litinin ne dattawan jihar Kano a karkashin kungiyar hadin kan Kano, ta yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar ganduje da ya janye dokar kirkirar karin masarautu a jihar.

A takardar da aka fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Tofa, tare da wasu dattawa goma kuma suka mika ga manema labarai, dattawan sun nuna fushinsu a kan yunkurin gurbata tarihin masarautar na sama da shekaru 1000.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like