Kotu ta ce majalisar dokokin jihar Kano ba ta da ikon bincikar Ganduje


Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin cewa majalisar dokokin jihar bata da ikon bincika ko kuma gayyatar gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje bisa zargin aikata laifi da ake masa.

Ana dai zargin gwamnan da karbar na goro daga hannun wasu yan kwangila a wani fefan bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta wallafa

Alkalin kotun,mai sharia Ahmad Badamasi shine ya yanke wannan hukuncin ya yin zaman kotun na ranar Talata.

Ya ce ikon binkicen aikata manyan laifuka na hannun hukumar ƴansanda, EFCC da kuma hukumar ICPC.

Alkalin ya ce duba da kundin tsarin mulki, majalisar dokokin jihar tana da iko ne kawai wajen yin doka da kuma gyaran dokokin da ake da su amma bata da ikon abin da ya shafi akaita laifuka.

Muhammad Zubairu, shugaban kungiyar Lawyers for Sustainable Democracy in Nigeria shine ya shigar da kara gaban kotun.

Sauran wadanda da ake kara a shari’ar sun hada da shugaban kwamitin binciken,Baffa Babba Danagundi da kuma majalisar dokokin jihar.

Lauyan masu karar,Nuraini Jimoh ya yaba da hukuncin kotun na yau.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like