Kotu ta bayar da umarnin kama tsohon gwamnan jihar Niger


Babban kotun tarayya dake Minna ta bayar da umarni kama tsohon gwamnan jihar Niger, Muazu Babangida Aliyu da kuma tsohon shugaban ma’aikatan gwamnan,Umar Nasko.

Alkalin kotun, Aminu Aliyu ya kuma soke hukuncin beli da tunda fari aka bawa Aliyu da Nasko kan gazawar da su kai na girmama sammacin da kotun ta yi musu na su bayyana a gabanta.

Kotu ta umarci Aliyu da Nasko da su sake bayyana a gabanta ranar Alhamis bayan da aka canza alkalin da zai saurari shari’ar da ake musu ta yin almundahana da biliyan ₦1.9 mallakin gwamnatin jihar lokacin da suke rike da madafun iko.

Lauyansu ya gaza bayyana a gaban kotu.

Amma daga bisani lauyan tsohon gwamnan,Olajide Ayodele ya rubuta takarda inda ya nemi da a dage zaman shari’ar.

Kotun ta dage zaman shari’ar ya zuwa ranar 27 ga watan Mayu.


Like it? Share with your friends!

-1
72 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like