Kotu ta bawa Zakzaky izinin zuwa kasar Indiya a duba lafiyarsa


Wata babbar kotu dake zamanta a Kaduna ta yanke hukuncin cewa, Ibrahim Elzakzaky shugaban kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da aka fi sani da shi’a zai iya tafiya kasar Indiya domin a duba lafiyarsa.

Jagoran kungiyar ta shi’a dake tsare a hannun jami’an tsaro tun shekarar 2015 ya nemi kotun ta bashi izinin ya je a duba lafiyar sa.

Shi da maidakinsa Zeenat an kama su bayan da magoya bayansu suka yi arangama da jami’an sojoji a shekarar 2015.

Babban lauya,Femi Falana shine ya shigar da bukatar Zakzaky da Zeenat a gaban kotun dake neman bazu izinin zuwa a duba lafiyarsu.

Alkalin kotun,Dairus Khobo ya bada umarnin cewa ya kamata a a kyale shugaban kungiyar ta shi’a da kuma mai dakinsa da su je kasar waje neman magani amma kuma dole su samu rakiyar jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kuma na gwamnatin jihar Kaduna.

Ya ce dole shugaban na shi’a ya dawo gida Najeriya da zarar an sallame shi daga asibiti domin cigaba da fuskantar shari’a.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like