Kotu ta bawa EFCC,DSS, Ƴansanda kama Diezani cikin sa’o’i 72


Valentine Ashi,alkalin babbar kotun birnin tarayya Abuja ta umarci hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati, hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kuma sauran hukumomin tsaro da suka kama Diezani Alison Madueke tsohuwar ministar mai cikin sa’o’i 72.

A cewar Tony Orilade mai magana da yawun hukumar ta EFCC umarnin ya biyo bayan bukatar kulawar gaggawa da lauyan EFCC, Msuur Denga ya shigar gaban kotun.

Denga ya roki kotun da ta bayar da izinin kama Madueke domin hukumar ta samu damar kamawa da kuma gurfanar da ita gaban kotu bisa zargin da ake mata na aikata cin hanci da rashawa.

A ranar Litinin kotun ta amince da bukatar EFCC ta a gurfanar da Madueke gabanta bayan da lauya mai gabatar da kara Faruk Abdullahi ya fadawa kotun cewa tsohuwar ministar ta fita daga kasarnan lokacin da ba a kammala bincike ba

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like