Kotu ta bada umarnin tsare matar da ta dorawa maciji alhakin cinye miliyan ₦35 na hukumar JAMB


Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin tsare,Philomina Chieshe da kuma wasu mutane biyar dake aiki hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya wato Jamb.

An bayar da umarni tsare su ne ranar Juma’a kan hannu da ake zargin suna da shi a bacewar naira miliyan 35 na sayar da katin karramawar Jamb a jihar Benue.

Chieshe ta gurfana a gaban kotun tare da Samuel Umoru, Yakubu Jekada, Daniel Agbo, Priscilla Ogunsola, and Aliyu Yakub

Hukuma EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ita ce ta gurfanar da mutanen kan tuhume-tuhume guda takwas da suka hada da kin fito da kudin hukumar tsakanin shekarar 2014-2016.

Peter Afen alkalin da ya jagoranci zaman shari’ar ya bayar da umarnin a cigaba da tsare wadanda ake zargi a hannun hukumar EFCC har zuwa lokacin yanke hukunci kan belin da suka nema.

EFCC ta yi zargin cewa Chieshe ta fadawa shugaban hukumar ta Jamb lokacin da ya kai ziyarar duba aiki cewa baza ta iya bayyana inda naira miliyan 35 suka shiga na katin jarrabawar hukumar da ta sayar a shekarun da suka gabata kafin a soke tsarin sayar da katin.

Jami’an sunyi zargin cewa tayi ikirarin maciji ne ya cinye kudin a Makurdi.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like