KOTU TA BADA UMARNIN CAFKE OKOCHA BISHA ƘIN BIYAN HARAJI


Wata babbar kotun jihar Legas da ke zamanta a Igbosere ta bayar da sabon umarnin a kama tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles), Augustine Okocha, bisa kin biyarn haraji.

Alkalin kotun ya bayar da sabon umarnin ne bayan babban mai gurfanar da jama’a a jihar Legas, Mista Yusuf Sule, ya roki kotun ta kara sabunta hukuncin da ta fara yanke wa a kan Okocha tun ranar 29 ga watan Janairu.

Sule ya shaida wa kotun cewar Okocha ya ki cika alkawarin sulhunta wa da hukuma, kamar yadda aka yi yarjejeniya a baya, a kan tuhumarsa da laifin kin biyan haraji a shekarar 2017.

Kazalika, ya ce Okocha ya ki bayyana a kotun tun bayan zuwansa na farko a ranar 5 ga watan Oktoba na shekarar 2017.

Sai dai, Okocha bai halarci kotun ba kuma babu wani lauya da ke kare shi da ya halarci zaman kotun.

Sule ya kara da cewa Okocha ya tuntubi hukumar tattara haraji ta jihar Legas (LIRS) amma har yanzu bai biya ko sisi ba.

Yace ” Wanda ake karar ya nuna niyyar biyan kudin, amma har yanzu bai bayar da ko sisi ba
“A saboda haka ne muke son kotu ta kara sabunta hukuncinta na farko, ” a cewar Sule.

Da ya ke amince wa da bukatar Sule, alkalain kotun, Akintoye, ya ce: ” umarnin neman a kamo wanda ake kara yana nan daram.
“An daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu.”

An fara shigar da karar Okocha ne a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2017, bisa zarginsa da aikata laifuka masu nasaba kauce wa biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas.


Like it? Share with your friends!

-1
78 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like