Kotu Ta Bada Belin Maryam Sanda


Wata kotu da ke zamanta a Jabi cikin babban birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Yusuf Halilu ta ba da belin Maryam Sanda wanda ake tuhuma da zargin kashe minjinta Bilyaminu Bello Halliru.

Har ila yau mai shari’ar ya bayyana ranar 19 ga watan nan da muke ciki a matsayin ranar da za a sake sauraren shari’ar.

Ba da belin Maryam ya biyo bayan bukatar da babban lauya Cif Joseph Dauda ya ba da na cewa tana dauke da ciki fiye da wata uku da kuma ciwon Asma kamar yadda sakamakon likitoci ya tabbatar.

Sai dai jami’in hukumar ‘yan sanda mai kula da shari’ar CSP James Idachaba ya soki lamirin ba da belin inda ya ce an yi shi ba bisa ka’ida ba.

Daga karshe mai shari’a Halilu ya ce. “jami’an ‘yan sanda ba su da hurumin kula da lafiyar Maryam, sannan kuma Maryam za ta kawo mutane ne biyu da za su tsaya mata wadanda suka mallaki wata kaddara a Abuja, kuma ya bukaci mahaifin Maryam da ya kasance cikin wadanda za su maido ta kotu a ranar shari’a mai zuwa”.


Like it? Share with your friends!

2
78 shares, 2 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like