Kotu Ta Amince A Ci Gaba da Shirin Yi Wa Dino Melaye KiranyeWata kotun tarayya da ke Abuja ta nemi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta kan ta ci gaba da shirye shiryen da ta fara na yi wa dan majalisar dattawan mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Maleye Kiranye bisa bukatar al’ummar mazabarsa.

Tun da farko dai, dan majalisar ya garzaya kotu inda ya nemi a dakatar da hukumar zabe kan shirin yi masa Kiranye bayan da gwamnatin jihar ta sanar da cewa ta samu sa hannun al’ummar mazabar Kogi ta Yamma wadanda suke neman a yi wa dan majalisarsu Kiranye a watan Yuni.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like