Kotu sauraran karar zaben shugaban kasa ta yi watsi da buƙatar Atiku


Kotun Sauraren Karar Zaben Shugaban Kasa, ta yi watsi da bukatar jam’iyar PDP da kuma Atiku Abubakar suka shigar gabanta dake neman a basu damar binciken na’urar ajiye bayanai ta hukumar INEC da aka yi amfani da ita a zaben shekarar 2019.

PDP da Atiku sun roki kotun da ta umarci hukumar ta basu damar bincikar na’urar ajiye bayanai da kuma sauran kayayyakin fasaha da aka yi amfani da su ya yin zaben na shugaban kasa.

Hukumar zaben ta mayar wa da martani ta hanyar cewa bata da na’urar ajiye bayanai inda ake tattara sakamakon zaben shugaban kasa.

Bukatar da dan takarar jam’iyar adawa ta PDP da kuma jam’iyar suka shigar anyi watsi da ita ne ya yin zaman kotun na ranar Litinin.


Like it? Share with your friends!

1
92 shares, 1 point

Comments 4

Your email address will not be published.

  1. Write a comment *BABA ATIKU WAZIRIN ADAMAWA DAZAKAYI HAKURI NE DA KADARA TA UBANGIJI AMASTAYINKA NA UBA AKASA KUMA DATTIJO MAI MUTUNCI MAI KAMALA MASANIN YAKAMATA DA KAHAKURA KAYI MUBAYA,A WA DAN UWANKA YAYANKA MUHAMMADU BUHARI TUN DA ALLAH YABASHI KATAIMAKE SHI DA SHAWARA MASUKYAU A MASAYINKA DAN KASA NAGARI MAI KISHIN KASA

You may also like