Wata kotun majistire dake Abuja ta bayar da umarnin tasa keyar wasu mutane su shida ya zuwa gidan yari.

Mutanen na daga cikin masu zanga-zangar EndSARS da suka sake tattaruwa domin cigaba da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja ranar Juma’a.

Masu zanga-zangar sun fara tattaruwa a hanyar shiga majalisar kasa domin cigaba da zanga-zangar da aka fara ta cikin watan Oktoba.

Amma sai jami’an yan sanda suka yi amfani hayaki mai sa hawaye da kuma harbin bindiga wajen tarwatsa su.

Yan sanda sun gurfanar da su gaban kotun inda suke musu tuhume-tuhume da da dama ciki har da kokarin tunzura mutane su tayar da tarzoma.