Ko kun san mata nawa Adam Zango ya taba aura a rayuwarsa?


Shahararren dan wasan Kannywood,Adam Zango ya shirya daura aure a karo na shida tun daga lokacin da ya daura auren farko a shekarar 2006.

Wannan ne dai karo na shida da jarumin yake aure bayan da ya saki ragowar matan da ya aura a baya.

Har kawo yanzu babu ɗaya daga cikin tsofaffin matan jarumin da ta fito fili ta bayyana dalilan rabuwar su.

A kasari mutane suna ganin Zango a matsayin namiji dake da dabi’ar nan ta auri saki.

Shafin Arewa24news.com ya gudanar da bincike kan matan da ya aura a baya da kuma ya’yan da kowace ta haifa masa.

1. Amina

Itace matar da Zango ya fara aure a shekarar 2006 inda kuma ta haifa masa dansa na fari da ake kira da “Haidar”a yanzu haka Haidar na da shekaru 12 da haihuwa kuma tuni ya fara bin sahun mahaifinsa ta hanyar fitowa a wasu fina-finai da kuma wakoki.

2.Aisha

Ita ce matar jarumin ta biyu wacce ya aura a Shika dake Zariya a jihar Kaduna kuma Allah ya albarkaci aurensu da yaya maza uku kafin rabuwar su.

3. Maryam

Mace ta uku da jarumin ya aura ita ce Maryam daga jihar Nasarawa.

4.Maryam Yola

Maryam AB Yola ita ce mace ta uku da jarumin ya aura a shekarar 2013 bayan da suka fito tare a fim din Nass.

5.Ummul Kulsum

Aure-auren na Zango bai tsaya a iya kasa Najeriya ba har sai da ta kai ya tsallaka kasar Kamaru Lardin Ngaoundere inda a cikin sirri aka daura masa aure da Ummul Kulsum inda ta haifa masa ya mai suna Murjanatu.

Abin jira a gani ko wannan auren da zai yi da amaryarsa Safiya Umar Chalawa wacce akafi sani da Suffy zai dore har tsawon rayuwar ma’auratan biyu? lokaci ne kadai zai iya tabbatar da haka.

Za a daure auren ne ranar Juma’a a babban masallacin Juma’a dake Gwandu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like