Kisan Gillar Janal Alkali: An Kama Matar Da Ta Jagoranci Zanga-zangar Hana Yashe Rafin Da Aka Gano Motar Sa


Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ce matar nan Rabecca Gyang da ta jagoranci mata sanye da bakaken kaya don hana yashe tabkin Dura Du don neman wa imma mota ko gawar marigayi Idris Alkali na hannun ta kuma a na ci gaba da gudanar da bincike.

Rabecca dai matar mai anguwar Latiya ce a yankin Du ami suna Pam Gyang Dung. Kazalika rundunar na rike da Stephen Chuwang da ya amsa ya na daga cikin wadanda su ka sauyawa gawar Idris Alkali waje daga ramin da su ka sanya shi zuwa wata tsohuwar rijiya a Guchwet.

Jami’in labarun rundunar ‘yan sandan na Filato Tyopez Terma ya ce za su gurfanar da mutum 13 gaban kotu don tuhumar da hannu a lamarin kisan gilla da Idris Alkali.

Hakanan Tyopev Terma ya ce tuni kwararru sun dauki kwayar halittar marigayin don gudanar da gwaji gabanin yi ma sa jana’iza a asabar din nan da ta gabata a Abuja.


Like it? Share with your friends!

-1
176 shares, -1 points

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like