Ke Duniya: Wani Matashi Ya Yiwa Budurwar Shi Yankan Rago A Jihar Yobe


Ana zargin wani matashi dan garin Potiskum dake jihar Yobe mai suna Muhammad Isa Adamu da yi wa budurwasa mai suna Hauwa yankan rago.

A bisa bayanan da iyayen Hauwa mazauna garin Damaturu suka yi, sun ce a ranar 29/05/2018 Hauwa ta fita da safe da niyyar sayo biredi a shago mafi kusa da su, sai dai tun daga fitar ta ba ta dawo ba har zuwa yammaci, wannan dalilin ya sa suka bazama nemanta, yayin da suka bada cigiyar ta a gidajen rediyo da ma wajen ‘yan sanda.

Kwatsam sai suka ji an samu gawar wata budurwa a kan titin Gujba, inda ba su yi kasa a guiwa ba zuwa wurin inda suka tabbatar da ‘yarsu ce.

A yayin da wannan matashi yake karin haske akan abun da ya faru, ya shaidawa manema labarai a garin Damaturu cewa, ya gayyaci Hauwa tsohuwar budurwarsa wadda ya fara nemanta tun 2014, soyayyarsu tayi nisa sosai, kuma bai taba sa ta wani abu ta ki yi ba, ya tabbatar da irin biyayya da Hauwa take masa, wannan dalilin yasa da ya gayyace ta kan hanyar Gujba, ba ta yi masa jayayya ba.

A cewar sa, bayan sun gama hirar su da Hauwa, sai ya umarce ta da ta rufe idonta, ba ta yi jayayya ba nan take ta rufe idon ta ba tare da ta san me yake shirin yi mata ba, sai ya ciro wuka ya soke ta a wuya, bada wani bata lokaci ba rai ya yi halinsa.

Da aka tambaye shi ko mai ya yi zafi har ya yanke wannan danyen hukunci ga wadda yake so?

Sai ya ce, ya yi iya kokarin sa don ganin mahaifansa su je Damaturu su nema masa auren Hauwa amma sun ki, kwatsam sai ya ga wani matashi ya fara zuwa wajen ta, wannan dalilin ya sa ya yanke hukuncin kashe ta kowa ma ya rasa.

A bisa bayanan da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Yobe ya yi wa manema labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin nan bada jimawa ba za su gurfanar da wannan matashi gaban kotu dan yanke masa hukunci.


Like it? Share with your friends!

-1
86 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

  1. Kai duniya ina zaki damu allah ya kyauta na ga ba amma wannan shi ma hunkucin kisa ya dace da shi tunda baida i mani wlh

You may also like