KAWU SUMAILA YA YI MURABUS DAGA MUKAMIN SA NA MASHAWARCIN SHUGABAN KASA.


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin Alhaji Abdurrahman Kawu Sumaila da Alhaji Ibrahim Umar El-Yakub a matsayin mai bashi shawara kan harkokin majalisa, bangaren majalisar wakilai ta kasa.

Wata sanarwa da Femi Adesina mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai ya fitar dazun nan ta bayana cewa an nada El-Yakub ne a matsayin saboda a jiya aikin da shi Kawu Sumaila din ya yi don shiga takarar majalisar wakilai ta kasa a mazabar Sumaila/Takai.

Shugaban kasar ya dai nada Alhaji Abdurrahman Kawu Sumaila ne a wannan mukami a watan Agusta na shekarar 2015.

Wanda ya gaji Kawu Sumaila din, Alhaji Ibrahim Umar El-Yakub wanda aka yiwa lakabi da (Kosasshe) ya taba kasancewa dan majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar birnin Kano a shekarar 2003 zuwa 2007,


Like it? Share with your friends!

1
89 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like