A wannan Litinin a Ingila ake janye kusan daukacin matakan da aka saka na yaki da yaduwar annobar cutar coronavirus. Wannan mataki zai haifar da walwala gami da rashin fuskantar bin matakan yaki da cutar da aka saba, sai dai haka ya haifar da tsoro tsakanin masana kimiyya gami da yanayin sauran sassan Birtaniya.

Firaministan Boris Johnson na Birtaniya da ministan lafiya Sajid Javid sun ce duk da tirjiya daga masana babu makawa wajen janye matakan da aka saka na yaki da cutar coronavirus daga wannan Litinin. Sai dai a cewar magajin garin birnin London Sadiq Khan za a ci gaba da saka kyallen rufe baki da hanci a cikin motocin safa-safa da manyan shagunan birnin.