Kason farko na alhazan jihar Katsina sun dawo gida


Kason farko na alhazan jihar Katsina su 495 sun sauka filin jirgin saman Umaru Musa Yar’adua, lafiya bayan sun kammala aikin hajjin bana.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa alhazan sun sauka a filin jirgin saman da misalin karfe 05:30 na safe cikin jirgin kamfanin Max Air.

Alhazan da suka fito daga kananan hukumomin, Dutsinma, Kankia,Mani da Daura sun dawo tare da kayansu.

Wasu daga cikin alhazan sun nuna godiyarsu ga Allah da ya dawo da su gida lafiya suka kuma yabawa hukumar alhazan jihar kan yadda ta kula da su yayin aikin hajin.

Daya daga cikinsu, Alhaji Aliyu Abdullahi ya godewa Allah bisa damar da ya basu ta kasancewa cikin wadanda suka yi aikin hajjin bana.

Abdullahi ya godewa gwamnatin jihar bisa kokarinta na ciyar da alhazan da kuma sama masu masauki mai kyau da kuma gudummawar ₦30,000 da ta bawa kowane Alhaji.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like