Kaso 95 na jihohi baza su iya biyan ₦30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi -David Umahi


Gwamnan jihar Ebonyi,David Umahi ya ce kaso 95 na jihohin dake kasarnan baza su iya biyan ₦30,000 ba a matsayin mafi ƙarancin alabashi ba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito Umahi na fadin haka ranar Laraba a Abakaliki babban birnin jihar.

Ya ce za iya biyan ₦30000 ne kaɗai idan aka sauya yadda ake rabon tattalin arzikin kasa ta yadda za a karawa jihohi abinda ake basu.

Gwamnan ya ce “gwamnatin tarayya tana karbar kaso 52 na kudin dake taruwa a asusun tarayya da nayi kokarin kara ₦30000 kan kananan hukumomi hakan na nufin sai sunci bashin biliyan ₦1 sun kara akan kasonsu wajen biyan albashi.

“Tabbas bazan zama gwamnan da zai mulki jiha irin haka ba bazan taba jagorantar jihar da zata ware kaso 100 na abin da ta ke samu ba wajen biyan albashi.”


Like it? Share with your friends!

2
135 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like