Kashe-Kashen Zamfara Ya Fi Na Binuwai Da Taraba Muni – Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kashe-kashen rayukan al’ummar da ake yi a jihar Zamfara ya zarce na jihohin Binuwai da Taraba munana, amma kuma an fi kwarmato, kwarototo da zuzuta na Jihohin Tarabar da Binuwai saboda tsananin kabilancin yare da na addini.

Shugaban kasar ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin din Arise.

Bayan nan Buhari ya shawarci kafofin yada labarai da su dinga watsa labaran gaskiya kuma sahihai ga al’umma ba irin wadanda ake gurbata su da son zuciya da kabilanci ba. Ya bayyana cewar ‘yan jarida suna da rawar takawa gurin tabbatuwar kasar nan cikin lumana ta hanyar nema tare da watsa sahihannin rahotanni na gaskiya da adalci.

Shugaban kasa ya zargi shuwagabannin jihohin Taraba da Binuwai kan zuzutawa tare da fitar da rahotannin karya domin tsabar kabilancin yare da na addini, inda ya ce in ma ka hade yawan mutanen da aka kashe a jihohin guda biyu basu kamar kafar na Zamfara ba.

“Dalilin shi ne gaba dayan mutanen da aka kashe a Taraba da Binuwai in ka hada su ba za su kai yawan wadanda aka kashe a jihar Zamfara ba. Amma rahoton da shuwagabannin Binuwai da Taraba suke fitarwa kabilancin yare da na addini ne kawai, kuma hakan rashin adalci ne ga Nijeriya,” Buhari ya fada.

Daga karshe shugaban kasa ya ce suna kan matukar kokarin samar da kyakkyawan tsaro a jihar Zamfara. Ya kara da fadin akwai matakai da yawa da suka dauka, ciki har da sauya dukkan ‘yan sandan da suka zarce shekaru uku suna aiki a jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like