Kashe-kashen Zamfara :Masarautar Anka ta yi kira da ayi azumi na kwanaki 3


Masarautar Anka dake jihar ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki tare da umartar al’umma da su yi azumin kwanaki uku domin Allah ya kawo musu dauki bisa matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Wasu yan bindiga a ranar Laraba sun kai hari kan kauyukan Kuru-kuru da Jarkuka inda suka kashe mutane 26 tare da jikkata wasu da dama.

Makonnin da suka gabata mutanen da basu gaza 30 ne ba aka kashe a wani hari makamancin wannan da aka kai kan kauyen Bawan Daji dake yankin.

Wazirin Anka, Alhaji Muhammad Inuwa, ya fadawa manema labarai a garin cewa daukar matakin ya biyo bayan ganawar da aka yi tsakanin fadar masarautar da kuma masu ruwa da tsaki dake yankin.

“Mun gudanar da ganawa da dama da mutanen mu da kuma masu ruwa da tsaki dake masautar Anka. Mun ayyana kwanaki uku na zaman makoki,”ya ce

“Haka kuma mun shawarci mutanen mu da su yi azumi na kwanaki uku na neman Allah ya yi maganin matsalar tsaro a yankin.”


Like it? Share with your friends!

-1
91 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like