Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira ga Isra’ila da Falasdinawa, da su kai zuciya nesa su rungumi shirin tsagaita wuta.

A wani sakon Twitter da ya wallafa a ranar Litinin, Jonathan ya ce kamata ya yi kasashen duniya sun mayar da hankali wajen sasanta tsakanin bangarorin biyu ba a rika ruruta rikicin ba.

“Ina kira ga kasashen duniya, da su mayar da hankalinsu wajen kashe wutar rikicin, ba ruruta ta ba.” Jonathan ya ce.

Ya kara da cewa, “abin da ake bukata cikin gaggawa shi ne tsagaita wuta, sai kuma samar da daidaito da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu.”

A cewar tsohon shugaban Najeriya, “abin da ya kamata kasashen duniya su mayar da hankali akai kenan – zaman lafiya, abu ne da zai yiwu.”

Jonathan ya kara da cewa, “na taba zuwa duka yankunan Isra’ila da Falasdinu, hakan ya ba ni damar fahimtar abubuwan da kowane bangare ke fuskanta.”

Tun da aka fara tarzomar a ranar 10 ga watan Mayu, akalla Falasdinawa 197 aka kashe ciki har da yara kanana 58 da mata 34 a cewar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin Gaza.

Akalla Yahudawa 10 aka kashe a hare-haren roka da aka harba a yankin, ciki har da yaro dan shekara shida.