Kasar Uganda Zata Aika Da Dakarun Soji Zuwa Sudan Ta Kudu Kasashen Uganda da Sudan Ta Kudu sun cimma yarjejeniya da za ta bawa Sojojin Uganda damar komawa Sudan Ta Kudu.

Za’a tura  Sojojin na Uganda kan babbar hanyar da ta hada babban birnin kasar Kamfala da kuma Juba babban birnin kasar Sudan Ta kudu.

 Rahoton yakara da cewa shugaban kasar Uganda ,Yoweri Museveni da takwaransa na Sudan Ta Kudu Salva Kirr sun kuma amince da a tura sojojin a wuraren da suke kawo barazana ga gwamnatin ta Sudan Ta Kudu. 

 Yarjejeniyar na zuwa ne bayan   kungiyoyin yan tawaye dake kudancin Sudan suka  tsaurara hare-haren da suke kaiwa  a kudancin kasar wanda hakan ke kawo tarnaki ga manyan motocin da suke kai kayayyaki kasar.

Kasar Uganda itace babbar abokiyar kasuwancin kasar Sudan Ta Kudu, koda a kwanakin baya sai da yan kasuwar kasar su kayi kira ga shugaba Museveni da yabada umarnin a kai sojoji kan hanyar da ta hada manyan biranen kasar biyu. 

Comments 0

Your email address will not be published.

Kasar Uganda Zata Aika Da Dakarun Soji Zuwa Sudan Ta Kudu 

log in

reset password

Back to
log in