Kasar Saudiyya Ta Bayar Da Tallafin Buhunan Abinci 140,468 Ga Najeriya


Masarautar Saudiyya ta hannun cibiyar bayar da tallafi na Sarki Salman ta bayar da tallafin buhuhunan abinci ga yan gudun hijirar da harin Boko Haram ya rutsa da su a jihohin Borno da Yobe.

Da yake jawabi a wajen rabon kayyakin sansanin kauyen Teacher, Maiduguri, jihar Borno, darakta janar na hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa, Injiniya Mustapha Maihaja ya bayyana cewa za’a raba Kwando 125,317 na kayayyakin abincin ga gidaje 33,343 a sansanoni da al’umman jihar Borno na tsawon watanni hudu masu zuwa.

Maihaja ya yabawa kokarin ministan tsaro ritaya birgediya janar Mansur Dan Ali wanda ya taimaka da abinci a yankin arewa maso gabas.

A borno ana rabon buhuhunan shinkafa da wake girman 25kg guda 125,372 da kuma kwalayen kayan dandanon abinci 62,686 kai tsaye da taimakon hukumomin NEMA, SEMA da kuma masu ruwa da tsaki.

Kakakin NEMA, Sani Datti yayi bayanin cewa a kowane gida mai dauke da mutane shida za su samu kwandon abinci na 59.8kg na tsawon wata guda.

Shugaban tawagar, mataimakin darakta na hukumar agaji daga cibiyar tallafi na sarki Salman, Naseer Alsubaie yace tallafin zai amfani yan gudun hijira sama da 840,000 a yankin arewa maso gabas.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like