Kasar Rasha Za Ta Fara Kallon ‘Yan Jarida A Matsayin ‘Yan Leken Asiri


Majalisar dokokin kasar Rasha ta gabatar da wani daftarin doka da zai mayar da ‘yan jaridun da ke yi wa kamfanonin kasashen waje aiki a matsayin ‘yan leken asirin kasa.

Wannan ya biyo matakin da bangaren zartarwar kasar ya dauka a bara na sanya wakilan kamfanonin yada labaran kasashen wajen a matsayin ‘yan leken asiri.

Mataimakin shugaban Majalisa, Pyotor Tolstoy ya ce, idan aka amince da wannan doka, za ta tilasta wa ‘yan jaridan bayyana in da suke samun kudadensu da kuma yadda suke kashe su.

Ana kallon dokar a matsayin mayar da martani kan Amurka wadda ita ma ta yi irinta domin bayyana ‘yan jaridun Rasha a matsayin ‘yan leken asirin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like