Kasar Rasha ta samar da maganin Korona mai inganci har an yi gwaji kan diyar shugaban kasa ta warke


Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da cewa kasar sa ta samar da rigakafin annobar korona kuma har an gwada maganin akan yarsa kuma ta warke tangaras.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta kai tsaye da yayi da kafafen talbijin din kasar.

Manuniya ta ruwaito yanzu haka an soma shirin yin gwajin maganin a kan daruruwan mutane kafin a soma fitar dashi sauran kasashe

Putin ya ce maganin mai inganci ne kuma shi ne irinsa na farko a duniya


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like