Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta hana . mutanen kasashen musulmi 13 takardar biza


Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da bada takardar izinin shiga kasar wato biza ga mutanen wasu kasashe 13 da galibinsu na musulmi ne da suka hada da Iran Turkiya,Syria da kuma Somalia

Sai dai dakatarwar zata kasance ta wucin gadi ya zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba.

Sanarwar da kasar ta fitar ta bayyana cewa an dakatar da bayarda biza ga mutanen da suka fito daga kasashen Algeria,Yemen, Lebanon, Iraq, Pakistan da Tunisia.

Sauran kasashen sun hada da Libiya,Kenya Tunisia da kuma Afghanistan.

Matakin na baya-bayan ya kawo ce-ce-ku-ce sosai a kafafen sadawar zamani.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like