Kasar Guinea ta rabu da annobar Ebola | Labarai | DWHukumar Lafiya ta Duniya da gwamnatin Guinea Conakry sun sanar da kawo karshen zagaye na biyu na annobar Ebola , ‘yan watanni kalilan bayan sake bullarta a wannan kasa ta yammacin nahiyar Afirka.  Ministan lafiya na Guinea Rémy Lamah da wani jami’in WHO, Alfred Ki-Zerbo ne suka yi shelar ayyana karshen Ebola a Guinea, a lokacin wani bikin hadin gwiwa a garin Nzérékoré inda cutar ta sake bayyana a karshen watan Janairu.

Akalla mutane 23 ne dai suka kamu da cutar ta Ebolar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, a cewar bayanin da WHO ta fitar a ranar Asabar.  Hukumomin na Guinea da na duniya sun yi saurin shawo kan annobar ta Ebola idan aka kwatanta da wacce aka yi fama da ita tsakanin 2013 zuwa 2016, inda ta yadu zuwa kasashen Laberiya da Saliyo. 

A wancan lokaci dai, sama da  mutane 11,300 suka kamu da Ebola, galibinsu a Guinea da Laberiya da Saliyo, da suka kasance a rukunin kasashe mafi talauci a duniya.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg