Kasar Faransa Ta Lashe Gasar Cin Kofin Duniya


Kasar Faransa ta kasance zakara a gasar cin kofin duniya na wannan shekarar ta 2018 wanda aka gudanar a kasar Rasha. An buga wasan karshe tsakanin Kasar Faransa da takwararta ta kasar Kuroshiya inda faransa ta samu nasara da ci 4 da 2.

Dan wasan karar faransa, Kylian Mbappe Ya kasance dan wasa dan kasa da shekaru 20 wanda yafi kowa hazaƙa a wasar, sai kuma dan wasan daya kasance shine mafi kokari A gasar wato Luka Modric na kasar Kuroshiya wanda yake taka leda a kulub din Real Madrid.

Sauran yan wasan da suka samu kyaututtuka sun hada da :

Harry Kane na kasar Ingila- yaci Kwallaye 6 wanda hakan ya bashi dama cin kyautar wanda yafi koaa zura kwallaye a gasar.

Thibo Courtois – mai tsaron ragar kasar Belgium wanda yake taka leda a club din Chelsea ya kasan Mai tsaron raga mafi hazaqa a gasar.

Sai kuma Spain daka kasance ƙasa mafi iya taka leda a wasan,


Like it? Share with your friends!

-1
76 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like