Kasar Chadi ta roki Najeriya ta samar mata da wutar lantarki


Gwamnatin kasar Chad a hukumance ta roki gwamnatin Najeriya da ta haɗa kasar da layin samar da wutar lantarki na Najeriya.

Jakadan kasar Chadi a Najeriya,Abakar Saleh Chachaimi shine ya gabatar da bukatar yayin wata ziyara da ya kai wa ministan wutat lantarki na Najeriya, Saleh Mamman a Abuja.

Da yake mayar da martani kan bukatar, Engr. Mamman ya yaba da da wannan cigaban da aka samu inda ya ce zai bunkasa alakar da ta dade a tsakanin kasashen biyu.

Ministan ya kara da cewa shekaru da dama kasarnan na samarwa da kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin hasken wutar lantarki.

Ya kuma kara da cewa bukatar tazo a lokacin da ya dace inda ya tabbatarwa da jakadan cewa Najeriya za ta saka bukatar a shirin da take na fadada layin dake rarraba hasken wutar lantarki.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like